L.Fir 20
20
Hukunci a kan Rashin Biyayya
1Ubangiji ya faɗa wa Musa, 2ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu. 3Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki. 4Idan kuwa mutanen ƙasar ba su kashe mutumin nan, wanda ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa ba, 5ni kaina zan yi gāba da mutumin nan da iyalinsa, da waɗanda suka yarda suka bi Molek tare da shi. Ba zan ƙara ce da su mutanena ba.
6“Duk wanda yake sha'ani da masu mabiya, ko da bokaye zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa. 7Sai ku kiyaye kanku da tsarki, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 8Ku kuma kiyaye dokokina, ku aikata su, gama ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.
9 #
Fit 21.17; Mat 15.4; Mar 7.10 “Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.
10 #
Fit 20.14; L.Fir 18.20; M.Sh 5.18 “Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar. 11#L.Fir 18.8; M.Sh 22.30; 27.20 Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu. 12#L.Fir 18.15 Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu. 13#L.Fir 18.22 Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu. 14#L.Fir 18.17; M.Sh 27.23 Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku. 15#Fit 22.19; L.Fir 18.23; M.Sh 27.21 Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar. 16In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.
17 #
L.Fir 18.9; M.Sh 27.22 “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu. 18#L.Fir 18.19 Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.
19 #
L.Fir 18.12-14
“Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi. 20Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa. 21#L.Fir 18.16 Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa.
22“Sai fa ku kiyaye dokokina duka, da ka'idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. 23Kada ku bi al'adun waɗannan al'ummai, waɗanda nake kora a gabanku, gama sun aikata waɗannan al'amura, don haka nake ƙyamarsu. 24Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai. 25Domin haka sai ku bambanta tsakanin halattattun dabbobi da haramtattun dabbobi, da tsakanin haramtattun tsuntsaye da halattattun tsuntsaye. Kada ku ƙazantar da kanku da haramtattun dabbobi, ko da tsuntsaye, ko da kowane abu mai rarrafe bisa ƙasa, waɗanda na ware su, su zama haramtattu a gare ku. 26Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa.
27“Namiji ko macen da yake da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”
Đang chọn:
L.Fir 20: HAU
Tô màu
Sao chép
So sánh
Chia sẻ
Bạn muốn lưu những tô màu trên tất cả các thiết bị của mình? Đăng ký hoặc đăng nhập
@Bible Society of Nigeria 1979