YouVersion Logo
Search Icon

Luk 6

6
Almajirai suna Zagar Alkama a Ran Asabar
(Mat 12.1-8; Mar 2.23-28)
1 # M.Sh 23.25 Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci. 2Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Don me kuke yin abin da bai halatta a yi ba a ran Asabar?” 3Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4#L.Fir 24.9#1Sam 21.1-6 Yadda ya shiga masujadar Allah, ya ɗauki keɓaɓɓiyar gurasan nan ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa, wadda ba ta halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai?” 5Sai ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”
Mai Shanyayyen Hannu
(Mat 12.9-14; Mar 3.1-6)
6A wata Asabar kuma ya shiga majami'a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye. 7Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 8Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin. 9Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?” 10Sai ya duddube su duke, ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa, hannunsa kuwa sai ya koma lafiyayye. 11Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.
Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu
(Mat 10.1-4; Mar 3.13-19)
12A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah. 13Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni. 14Su ne Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas, 15da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti, 16da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.
Yesu Ya Hidimta wa Mutane Masu Yawa
(Mat 4.23-25)
17Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu. 18Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su. 19Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
Albarka da La'ana
(Mat 5.1-12)
20Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,
“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.
21“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke.
“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.
22 # 1Bit 4.14 “Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum. 23#2Tar 36.16; A.M 7.52 Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.
24“Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta'aziyya.
25“Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa.
“Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.
26“Kaitonku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”
Ƙaunar Magabta
(Mat 5.38-48; 7.12)
27“Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri. 28Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a. 29Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma. 30Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi. 31#Mat 7.12 Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.
32“In masoyanku kawai kuke ƙauna wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu. 33In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi. 34In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai. 35Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye. 36Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”
Kada ku Ɗora wa Kowa Laifi
(Mat 7.1-5)
37“Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku. 38Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”
39 # Mat 15.14 Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba? 40#Mat 10.24,25; Yah 13.16; 15.20 Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa. 41Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba? 42Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, ‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”
Akan Gane Itace ta 'Ya'yansa
(Mat 7.16-20; 12.33-35)
43“Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan 'ya'ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan 'ya'ya. 44#Mat 12.33 Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya. 45#Mat 12.34 Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”
Kafa Harsashin Gini Iri Biyu
(Mat 7.24-27)
46“Don me kuke kirana, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku? 47Duk mai zuwa wurina, yake jin maganata, yake kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa. 48Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci. 49Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”

Currently Selected:

Luk 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy