YouVersion Logo
Search Icon

Fili 1

1
Gaisuwa
1 # A.M 16.12 Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.
2Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.
Addu'ar Bulus domin Filibiyawa Masu Bin Almasihu
3Ina gode Allahna duk sa'ad da nake tunawa da ku, 4a kullum kuwa a kowace addu'a da nake muku duka, da farin ciki nake yi. 5Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu. 6Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu. 7Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita. 8Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi. 9Addu'ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa, 10domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu, 11kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.
Manufar Rayuwata, Almasihu Ne
12'Yan'uwa, ina so ku sani, al'amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara, 13#A.M 28.30 har dai ya zama sananne ga dukan sojan fāda da sauran jama'a, cewa ɗaurina saboda Almasihu ne. 14Har ma galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.
15Lalle waɗansu suna wa'azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne. 16Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara. 17Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.
18Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Almasihu, na kuma yi farin ciki da haka. I, zan yi farin ciki kuwa. 19Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu. 20Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata. 21Domin ni, a gare ni, rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce. 22In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa. 23Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa. 24Amma in wanzu a cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku. 25Na tabbata haka ne, na kuwa sani zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku yin farin ciki, 26ku kuma sami ƙwaƙƙwaran dalilin yin taƙama da Almasihu ta wurina, saboda sāke komowata gare ku.
27Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa, 28ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam. Wannan kuwa ishara ce a gare su ta hallakarsu, ku kuwa ta cetonku, isharar kuwa daga Allah take. 29Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa, 30#A.M 16.19-40 kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.

Currently Selected:

Fili 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy