YouVersion Logo
Search Icon

Yah 12

12
An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya
(Mat 26.6-13; Mar 14.3-9)
1Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Betanya inda Li'azaru yake, wanda Yesu ya tasa daga matattu. 2Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li'azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi. 3#Luk 7.37,38 Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man. 4Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bāshe shi, ya ce, 5“Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba talakawa kuɗin?” 6Ya faɗi haka fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a'a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da yake ciki. 7Sai Yesu ya ce, “A ƙyale ta, dā ma ta ajiye shi domin tanadin ranar jana'izata. 8#M.Sh 15.11 Ai, kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”
An Ƙulla Shawara Gāba da Li'azaru
9Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba domin Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li'azaru wanda ya tasa daga matattu. 10Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li'azaru, shi ma, 11domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.
Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu
(Mat 21.1-11; Mar 11.1-11; Luk 19.28-40)
12Kashegari babban taron da suka zo idi, da suka ji Yesu yana zuwa Urushalima, 13#Zab 118.25,26 suka ɗaɗɗauko gazarin dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila!” 14Da Yesu ya sami wani jaki sai ya hau, yadda yake a rubuce cewa,
15 # Zak 9.9 “Kada ki ji tsoro, ya ke 'yar Sihiyona,
Ga sarkinki na zuwa a kan aholakin jaki!”
16Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi.
17Taron da yake tare da shi sa'ad da ya kira Li'azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka. 18Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu'ujizan nan. 19Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”
Waɗansu Helenawa Sun Nemi Yesu
20To, a cikin waɗanda suka zo idin yin sujada akwai waɗansu Helenawa. 21Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Betsaida ta ƙasar Galili, suka roƙe shi suka ce, “Maigida, muna bukatar mu gana da Yesu.” 22Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu. 23Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. 24Lalle hakika, ina gaya muku, in ba an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa. 25#Mat 10.39; 16.25; Mar 8.35; Luk 9.24; 17.33 Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami. 26Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”
Lalle a Ɗaga Ɗan Mutum Sama
27“Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci’? A'a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci. 28Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,” 29Da taron da yake tsaye a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala'ika ne ya yi masa magana.” 30Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan muryan nan ba, sai dominku. 31Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan. 32Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.” 33Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi. 34#Zab 110.4; Ish 9.7; Eze 37.25; Dan 7.14 Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?” 35Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba. 36Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.”
Yahudawa Ba Su Gaskata da Shi Ba
Yesu ya faɗi haka, sa'an nan ya tafi ya ɓuya musu. 37Amma ko da yake ya sha yin mu'ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba, 38#Ish 53.1 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,
“Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?
Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?”
39Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa,
40 # Ish 6.10 “Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu,
Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci,
Har su juyo gare ni in warkar da su.”
41Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa. 42Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a. 43Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.
Maganar Yesu Za ta Yi Hukunci
44Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba da ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne. 45Wanda kuma yake dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. 46Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu. 47Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya. 48Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe. 49Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi. 50Na kuma san umarnin nan nasa rai ne madawwami. Domin haka, abin da nake faɗa ina faɗa ne daidai yadda Uba ya faɗa mini.”

Currently Selected:

Yah 12: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy