YouVersion Logo
Search Icon

Hag 1

1
An Zuga Mutane Su Gina Haikali
1 # Ezra 4.24—5.2; 6.14 A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. 2Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Mutanen nan suna cewa lokaci bai yi ba tukuna da za a sāke gina Haikalin Ubangiji.”
3Ubangiji kuwa ya yi magana da annabi Haggai ya ce, 4“Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi wa rufin katako, amma Haikalin nan yana zaman kufai? 5Yanzu, ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku lura da al'amuranku! 6Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.” 7Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku lura da al'amuranku! 8Ku haura zuwa kan tuddai, ku kawo itace don ku gina Haikalina, in ji daɗinsa, a kuma ɗaukaka ni.
9“Kun sa zuciya za ku sami da yawa, sai kuka sami kaɗan. Sa'ad da kuma kuka kawo shi gida, sai na hurar da shi. Me ya sa haka? Saboda Haikalina da yake zaman kufai, amma ko wannenku yana fama da ginin gidansa. 10Domin haka sama ta ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfani. 11Na kawo fari a kan ƙasa, da kan tuddai, da kan hatsi, da kan 'ya'yan inabi, da kan 'ya'yan zaitun, da kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da kan mutane, da kan dabbobi, da kan ayyukansu.”
12Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji. 13Sai Haggai, manzon Ubangiji, ya faɗa wa mutane maganar Ubangiji, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ni Ubangiji ina tare da ku.’ ” 14Ubangiji kuwa ya zuga zuciyar Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da zuciyar dukan sauran mutane. Suka zo, suka fara aikin Haikalin Ubangiji Allahnsu Mai Runduna 15a ranar ashirin da huɗu ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus.

Currently Selected:

Hag 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy