YouVersion Logo
Search Icon

Afi 1

1
Gaisuwa
1 # A.M 18.19-21; 19.1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.
2Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Albarku na Ruhu a Cikin Almasihu
3Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu, 4domin kuwa ya zaɓe mu a cikin Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa. 5Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri, 6domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa. 7#Kol 1.14 Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah, 8wanda ya falala mana. Da matuƙar hikima da basira 9ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu. 10Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.
11A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi, 12domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa. 13A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa'ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta. 14Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.
Addu'a don Hikima da Sani
15Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka, 16ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa'ad da nake yi muku addu'a, 17da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah, 18a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka, 19da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa, 20#Zab 110.1 wanda ya zartar ga Almasihu sa'ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya, 21a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma. 22#Zab 8.6#Kol 1.18 Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka. 23Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.

Currently Selected:

Afi 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy