YouVersion Logo
Search Icon

L.Ƙid 7

7
Hadayun Keɓe Bagade
1A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa. 2Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya, 3suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su, 4sai Ubangiji ya ce wa Musa, 5“Karɓi waɗannan daga gare su domin a yi aiki da su a alfarwa ta sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.” 6Musa kuwa ya karɓi karusan, da takarkaran, ya ba Lawiyawa. 7Ya ba 'ya'ya maza na Gershon karusai biyu da takarkarai huɗu bisa ga aikinsu. 8Ya kuwa ba 'ya'ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist. 9Amma bai ba 'ya'ya maza na Kohat kome ba, domin aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
10Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden, 11Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.” 12-83Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka,
Rana Kabila Shugaba
Rana ta farko Yahuza Nashon ɗan Amminadab
Rana ta biyu Issaka Netanel ɗan Zuwar
Rana ta uku Zabaluna Eliyab ɗan Helon
Rana ta huɗu Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur
Rana ta biyar Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai
Rana ta shida Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel
Rana ta bakwai Ifraimu Elishama ɗan Ammihud
Rana ta takwas Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur
Rana ta tara Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni
Rana ta goma Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai
Rana ta goma sha ɗaya Ashiru Fagiyel ɗan Okran
Rana ta goma sha biyu Naftali Ahira ɗan Enan
Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.
84-88Ga jimillar hadayun da shugabanni goma sha biyu suka kawo domin keɓewar bagaden:
farantan azurfa goma sha biyu da kwanonin azurfa goma sha biyu, duka nauyinsu shekel dubu biyu da ɗari huɗu
cokulan zinariya goma sha biyu, nauyinsu duka shekel ɗari da ashirin cike da kayan ƙanshi
bijimai goma sha biyu, da raguna goma sha biyu, da 'yan raguna goma sha biyu bana ɗaya ɗaya, da kuma hadaya ta gari da za a haɗa da waɗannan domin hadaya ta ƙonawa
awaki goma sha biyu domin hadaya don zunubi
bijimai ashirin da huɗu, da raguna sittin, da awaki sittin, da 'yan raguna bana ɗaya ɗaya guda sittin domin hadaya ta salama.
89Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.

Currently Selected:

L.Ƙid 7: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for L.Ƙid 7