YouVersion Logo
Search Icon

L.Ƙid 12

12
Aka Hukunta Maryamu
1Sai Maryamu da Haruna suka zargi Musa saboda mace, Bahabashiya, wadda ya aura. 2Suka ce, “Da Musa kaɗai ne, Ubangiji ya yi magana, bai yi magana da mu kuma ba?” Ubangiji kuwa ya ji. 3(Musa dai mai tawali'u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.)
4Farat ɗaya sai Ubangijiya ce wa Musa, da Haruna, da Maryamu, “Ku uku, ku tafi zuwa alfarwa ta sujada.” Sai su uku suka tafi. 5Ubangiji kuwa ya zo cikin al'amudin girgije, ya tsaya a ƙofar alfarwar, ya yi kira, “Haruna! Maryamu!” Su biyu fa suka gusa gaba. 6Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki. 7#Ibr 3.2Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama'ata Isra'ila. 8Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?”
9Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su. 10Sa'ad da al'amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa. 11Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta. 12Na roƙe ka kada ka bari ta zama kamar matacce wanda rabin jikinsa ruɓaɓɓe ne a lokacin da aka haife shi.”
13Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.”
14 # L.Ƙid 5.2,3 Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.” 15Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama'ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon. 16Bayan wannan jama'a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.

Currently Selected:

L.Ƙid 12: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in