L.Ƙid 1
1
Ƙidaya ta Farko a Jejin Sinai
1 #
L.Ƙid 26.1-51
A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce, 2“Da kai da Haruna ku ƙidaya Isra'ilawa, bisa ga kabilansu da iyalansu. Ku tsara sunayen dukan mazaje 3daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi. 4Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”
5-15Waɗannan su ne mutanen da aka zaɓa.
| Kabila | Shugaban Kabila |
|---|---|
| Ra'ubainu | Elizur ɗan Shedeyur |
| Saminu | Shelumiyel ɗan Zurishaddai |
| Yahuza | Nashon ɗan Amminadab |
| Issaka | Netanel ɗan Zuwar |
| Zabaluna | Eliyab ɗan Helon |
| Ifraimu | Elishama ɗan Ammihud |
| Manassa | Gamaliyel ɗan Fedazur |
| Biliyaminu | Abidan ɗan Gideyoni |
| Dan | Ahiyezer ɗan Ammishaddai |
| Ashiru | Fagiyel ɗan Okran |
| Gad | Eliyasaf ɗan Deyuwel |
| Naftali | Ahira ɗan Enan |
16Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama'a domin wannan aiki.
17Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu, 18suka kuma kira dukan jama'a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta, 19kamar yadda Ubangiji ya umarta.
Musa ya rubuta jama'a a jeji ta Sinai. 20-46Mazaje masu shekara ashirin ko fi da suka isa yaƙi aka rubuta su suna suna, bisa ga kabilansu da iyalansu, aka fara da kabilar Ra'ubainu, babban ɗan Yakubu. Ga yadda jimillarsu take.
| Kabila | Jimilla |
|---|---|
| Ra'ubainu | (46,500) Dubu arba'in da shida da ɗari biyar. |
| Saminu | (59,300) Dubu hamsin da tara da ɗari uku. |
| Gad | (45,650) Dubu arba'in da biyar da ɗari shida da hamsin. |
| Yahuza | (74,600) Dubu saba'in da huɗu da ɗari shida. |
| Issaka | (54,400) Dubu hamsin da huɗu da ɗari huɗu. |
| Zabaluna | (57,400) Dubu hamsin da bakwai da ɗari huɗu. |
| Ifraimu | (40,500) Dubu arba'in da ɗari biyar. |
| Manassa | (32,200) Dubu talatin da biyu da ɗari biyu. |
| Biliyaminu | (35,400) Dubu talatin da biyar da ɗari huɗu. |
| Dan | (62,700) Dubu sittin da biyu da ɗari bakwai. |
| Ashiru | (41,500) Dubu arba'in da ɗaya da ɗari biyar. |
| Naftali | (53,400) Dubu hamsin da uku da ɗari huɗu. |
| Jimilla duka | (603,550) dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin. |
An Ba Lawiyawa Ikon Alfarwa
47Amma ba a rubuta Lawiyawa tare da sauran kabilai ba, 48gama Ubangiji ya ce wa Musa, 49“Sa'ad da kake ƙidaya Isra'ilawa, kada ka haɗa da kabilar Lawi. 50A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita. 51Sa'ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi. 52Sauran Isra'ilawa za su sauka ƙungiya ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa a ƙarƙashin tutarsa. 53Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama'ar Isra'ila.” 54Sai Isra'ilawa suka aikata kowane abu da Ubangiji ya umarci Musa.
Currently Selected:
L.Ƙid 1: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: