L.Fir 25
25
Bikin Kewayowar Shekaru
1 #
Fit 23.10,11 Ubangiji kuwa ya yi wa Musa magana a kan Dutsen Sina'i, ya ce 2ya faɗa wa Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, ƙasar za ta kiyaye shekara ta bakwai ga Ubangiji. 3Shekara shida za su yi, suna ta noman gonakinsu, suna kuma ta aske gonakin inabinsu, suna tattara amfaninsu. 4Amma shekara ta bakwai ta Ubangiji ce, sh ekara ce ta hutawa ga ƙasar. Kada su nomi gonakinsu, ko kuwa su aske inabinsu. 5Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar. 6A shekarar nan ɗin ƙasar za ta tanada musu abinci, da su da bayinsu mata, da maza, da barorinsu na ijara, da baƙon da yake zaune tare da su, 7har da dabbobinsu na gida da na jeji. Duk albarkar da ƙasar za ta bayar, za ta zama abinci.
Murnar Shekara ta Hamsin
8Sai su ƙidaya shekara bakwai har sau bakwai. Shekarar nan bakwai sau bakwai su ne shekara arba'in da tara a gare su. 9A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka. 10Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa. 11Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara 'ya'yan inabin da ba su yi wa aski ba. 12Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar.
13Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa. 14In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna. 15Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. 16Idan shekarun sun ragu da yawa kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, sai ka saya da tsada. Idan kuwa shekarun sun ragu kima ne, sai ka saya da araha, gama yana sayar maka bisa ga yawan shekarun da za ka mora ne. 17Kada ku cuci juna fa, amma ku ji tsoron Allahnku, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”
Matsalolin Shekarar Murna
18“Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka'idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya. 19Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.
20“Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba, 21ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku. 22Sa'ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”
Fansar Mallaka
23“Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.
24“Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka. 25Idan ɗan'uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan'uwansa ya jinginar. 26Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa, 27to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa'an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa. 28Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa.
29“Haka nan kuma idan mutum ya jinginar da gida a cikin birni mai garu, yana da izini ya fanshi abinsa a ƙarshen shekara guda. 30Idan kuwa bai fanshi gidan a ƙarshen shekara guda ba, sai gidan nan da yake cikin birni mai garu ya zama mallakar wanda ya karɓi jinginar, da na zuriyarsa duka har abada. Ba za a mayar wa maigidan da gidan a shekara ta hamsin ta murna ba. 31Amma gidajen da suke cikin ƙauyuka da ba su cikin garu, sai a lasafta su daidai da gonakin da suke cikin ƙasar, ana iya fansarsu, za a kuma mayar wa masu su a shekara ta hamsin ta murna. 32Amma a kan biranen Lawiyawa, da gidajen da suke cikin biranen da suka mallaka, Lawiyawa suna da izini su fanshe su a kowane lokaci. 33Amma idan wani daga cikin Lawiyawa bai fanshi gidansa ba, a shekara ta hamsin ta murna sai a mayar masa da gidan nan na cikin birnin da suka mallaka, gama gidajen da suke cikin biranen Lawiyawa su ne nasu rabo a cikin Isra'ilawa. 34Ba za a jinginar da hurumin biranensu ba, gama wannan shi ne abin mallakarsu har abada.”
Ba da Rance ga Matalauci
35 #
M.Sh 15.7,8 “Idan ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce, ya kasa riƙon kansa, sai ka riƙe shi kamar baƙon da yake baƙunci a wurinka. 36Kada ka ba shi rance da ruwa, amma ka ji tsoron Allah ka bar ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya zauna tare da kai. 37#Fit 22.25; M.Sh 23.19,20Kada ka ranta masa kuɗi da ruwa, kada kuma ka ba shi abinci don samun riba. 38Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fanshe ku daga ƙasar Masar don in ba ku ƙasar Kan'ana, in zama Allahnku.”
'Yantar da Bayi
39 #
Fit 21.2-6; M.Sh 15.12-18 “Idan kuwa ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya talauce har ya sayar da kansa gare ka, to, kada ka bautar da shi kamar bawa. 40Amma ya zauna tare da kai kamar bara na ijara, ko kuwa kamar wanda yake baƙunci. Sai ya yi aiki tare da kai har shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. 41Sa'an nan shi da iyalinsa su rabu da kai, ya koma wurin danginsa da mahallin kakanninsa. 42Gama su bayina ne, waɗanda na fanshe su daga ƙasar Masar, ba za a sayar da su kamar yadda ake sayar da bayi ba. 43Kada ka mallake shi da tsanani, amma ka ji tsoron Allahnka. 44Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al'ummar da yake kewaye da ku. 45Kwa iya sayen bayi daga baƙin da yake baƙunci a wurinku, su da iyalinsu waɗanda aka haifa a ƙasarku. Kwa iya sayensu su zama dukiyarku. 46Kwa iya barinsu ga 'ya'yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma 'yan'uwanku, Isra'ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba.
47“Idan baƙo ne ko mai aikin ijara da yake zaune tare da ku ya arzuta, ɗan'uwanku kuwa wanda yake kusa da shi ya talauce, har ya sayar da kansa ga baƙon, ko mai aikin ijarar da yake tare da ku, ko kuwa ga wani daga cikin iyalin baƙon, 48bayan da ya sayar da kansa ana iya fansarsa. Wani daga cikin 'yan'uwansa ya iya fansarsa. 49Ko kawunsa, ko ɗan kawunsa, ko wani daga cikin danginsa na kusa ya iya fansarsa. Idan kuma shi kansa ya arzuta ya iya fansar kansa. 50Sai ya sa wanda ya saye shi ya lasafta tun daga shekarar da ya sayar da kansa, har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Ƙuɗin da za a fanshe shi zai zama daidai da yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta murna. Sai a ɗauke shi kamar bara na ijara. 51Idan shekarun sun ragu da yawa, sai ya fanshi kansa bisa ga adadin kuɗin da aka saye shi. 52Amma idan shekarun sun ragu kaɗan kafin shekara ta hamsin ta murna, sai ya lasafta, ya biya don fansarsa bisa ga yawan shekarun. 53Sai baƙon ya mai da shi kamar bara mai aikin ijara, shekara a kan shekara. Amma kada ya tsananta masa. 54Idan ba a fanshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, sai a shekara ta hamsin ta murna, a sake shi, shi da 'ya'yansa. 55Gama a gare ni Isra'ilawa bayi ne waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
Currently Selected:
L.Fir 25: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979