L.Fir 23
23
Ƙayyadaddun Idodi
1Ubangiji ya ba Musa 2waɗannan ka'idodi domin ƙayyadaddun idodi sa'a da Isra'ilawa za su taru domin yin sujada. 3#Fit 20.8-10; 23.12; 31.15; 34.21; 35.2; M.Sh 5.12-14 Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce. 4Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.
Idin Ƙetarewa da na Abinci Marar Yisti
(L.Ƙid 28.16-25)
5 #
Fit 12.1-13; M.Sh 16.1,2 Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji. 6#Fit 12.14-20; 23.15; 34.18; M.Sh 16.3-8Sa'an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai. 7Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba. 8A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.
9Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 10lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu. 11Firist ɗin zai kaɗa damin hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, don a karɓe su. Firist zai kaɗa hadayar a kashegarin Asabar. 12A ranar da suka miƙa hadaya ta kaɗawa, za su kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da ɗan rago bana ɗaya marar lahani. 13Tare da wannan hadaya kuma, za su miƙa hadaya ta gari, humushi biyu na garwar gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Za su kuma miƙa hadaya ta sha da ruwan inabi kwalaba ɗaya. 14Kada su ci sabon hatsin, wanda aka tuma, ko ɗanyensa, ko wanda aka yi gurasa da shi sai sun kawo hadayarsu ta sabon hatsi ga Allah. Za su kiyaye wannan ka'ida, da su da dukan zuriyarsu, har dukan zamanai masu zuwa.
Idin Girbi
(L.Ƙid 28.26-31)
15 #
Fit 23.16; 34.22; M.Sh 16.9-12 Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji. 16Kwana hamsin za su ƙirga zuwa kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa'an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji. 17Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji. 18Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 19Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama. 20Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da 'yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist. 21A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.
22 #
L.Fir 19.9,10; M.Sh 24.19-22 Sa'ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.
Idin Sabuwar Shekara
(L.Ƙid 29.1-6)
23Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 24ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada. 25Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
Ranar Kafara
(L.Ƙid 29.7-11)
26 #
L.Fir 16.29-34
Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa, 27rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji. 28Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu. 29Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama'ar Allah ba. 30Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi. 31Wannan ka'ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke. 32Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.
Idin Bukkoki
(L.Ƙid 29.12-40)
33 #
M.Sh 16.13-15
Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa, 34a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji. 35Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba. 36A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.
37Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta. 38Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa'adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji.
39A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, bayan da sun gama tattara amfanin gonakinsu, sai su yi idi ga Ubangiji har kwana bakwai. Rana ta fari, da rana ta takwas za su zama muhimman ranakun hutawa. 40A ranar sai su ɗibi 'ya'yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa'an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai. 41Za su yi idin nan ga Ubangiji har kwana bakwai. Wannan ka'ida ce a gare su har abada. 42Za su zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Duk 'yan ƙasa waɗanda suke Isra'ilawa za su zauna cikin bukkoki. 43Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra'ilawa su zauna cikin bukkoki, sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.
44Haka kuwa Musa ya sanar wa mutanen Isra'ila da ƙayyadaddun idodin Ubangiji.
Currently Selected:
L.Fir 23: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: