YouVersion Logo
Search Icon

Far 13

13
Rabuwar Abram da Lutu
1Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu. 2Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya. 3Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai, 4a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
5Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai, 6domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba. 7Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne.
8Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne. 9Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.” 10#Far 2.10 Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata. 11Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna. 12Abram ya zauna a ƙasar Kan'ana, Lutu kuwa ya zauna a biranen kwari, ya zakuɗar da alfarwarsa har zuwa Saduma. 13Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.
Abram Ya Yi Ƙaura zuwa Hebron
14Sai Ubangiji ya ce wa Abram, bayan da Lutu ya rabu da shi, “Ɗaga idanunka sama, daga inda kake, ka dubi kusurwoyin nan huɗu, 15#A.M 7.5 gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada. 16Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka. 17Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan ba ka ita.” 18Sai Abram ya cire alfarwarsa, ya zo ya zauna kusa da itatuwan oak na Mamre, waɗanda suke Hebron. A can ya gina wa Ubangiji bagade.

Currently Selected:

Far 13: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy