YouVersion Logo
Search Icon

2Sam 1

1
Dawuda Ya ji Labarin Rasuwar Saul da Jonatan
1Bayan rasuwar Saul, sa'ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag. 2Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa. 3Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”
Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra'ilawa.”
4Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”
Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”
5Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”
6 # 1Sam 31.1-6; 1Tar 10.1-6 Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi. 7Da ya waiga, ya gan ni, sai ya kira ni, ni kuwa na amsa, na ce, ‘Ga ni.’ 8Ya ce mini, ‘Wane ne kai?’ Na ce masa, ‘Ni Ba'amaleke ne.’ 9Sai ya ce mini, ‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.’ 10Sai na tafi na kashe shi domin na tabbata ba zai yi rai ba bayan ya fāɗi. Na kuma cire kambin da yake kansa da ƙarau da yake a dantsensa. Ga su, na kawo wa ubangijina.”
11Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu. 12Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra'ila domin an Karkashe su a yaƙi.
13Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?”
Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba'amaleke.”
14Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?” 15Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin samarin, ya ce masa, “Ka kashe shi.” Ya dai buge shi, ya mutu. 16Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”
Dawuda Ya Yi Makoki domin Saul da Jonatan
17Sai Dawuda ya raira waƙar makoki domin Saul da Jonatan, ɗansa. 18#Josh 10.13 Ya umarta a koya wa mutanen Yahuza wannan waƙa. (An rubuta ta a littafin Yashar.)
19“An kashe darajarki, ya Isra'ila, a kan tuddanki!
Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!
20Kada a ba da labarin a Gat,
Ko a titin Ashkelon.
Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna,
Kada ku sa 'yan matan arna su yi farin ciki.
21“Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa.
Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani.
Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance,
Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.
22Bakan Jonatan mai kisa ne,
Takobin Saul ba shi da jinƙai,
Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.
23“Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha'awa,
A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare.
Sun fi gaggafa sauri,
Sun fi zaki ƙarfi.
24“Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul!
Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa,
Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.
25“Jarumawa sun fāɗi,
An kashe su a bakin dāga.
Jonatan na kwance matacce a tuddai.
26“Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan'uwana Jonatan,
Ƙaunatacce kake a gare ni!
Ƙaunarka a gare ni abar al'ajabi ce,
Ta fi ƙaunar mace.
27“Jarumawa sun fāɗi,
Makamansu ba su da sauran amfani.”

Currently Selected:

2Sam 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy