YouVersion Logo
Search Icon

1Tim 1

1
Gaisuwa
1Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu, 2#A.M 16.1 zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya.
Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.
Faɗaka a kan Wata Koyarwa Dabam
3Kamar yadda na roƙe ka, ka dakata a Afisa sa'ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi waɗansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam, 4kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al'amuran Allah da bangaskiya. 5Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya. 6Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza. 7Suna burin zama masanan Attaura, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle matsalar da suke taƙamar haƙiƙicewa a kai.
8To, mun san Shari'a aba ce mai kyau, in mutum ya yi aiki da ita yadda ya wajaba, 9yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, 10da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan, 11bisa ga bishara mai daraja ta Allah abar yabo, wadda aka danƙa mini.
Godiyar Bulus domin Jinƙai
12Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijinmu, wanda ya ƙarfafa ni, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa, 13#A.M 8.3; 9.4,5 ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya. 14Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu. 15Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu. 16Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami. 17Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.
18Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau, 19kana riƙe da bangaskiya da lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20Cikinsu har da Himinayas da Askandari, waɗanda na miƙa wa Shaiɗan, don su horo su bar yin sāɓo.

Currently Selected:

1Tim 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy