YouVersion Logo
Search Icon

Mattiyu 3

3
Yohanna Mai Baftisma ya shirya hanya
(Markus 1.1-8; Luka 3.1-18; Yohanna 1.19-28)
1A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya 2yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.” 3Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa,
“Ga murya mai kira a hamada tana cewa,
‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,
ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”#3.3 Ish 40.3
4Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji. 5Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun. 6Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.
7Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. 9Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan. 10An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.
11“Ina muku baftisma da#3.11 Ko kuwa a cikin ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. 12Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
Baftismar Yesu
(Markus 1.9-11; Luka 3.21,22)
13Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma. 14Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”
15Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.
16Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa. 17Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”

Currently Selected:

Mattiyu 3: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy