1
L.Fir 26:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Zan yi tafiya tare daku, in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena.
Compare
Explore L.Fir 26:12
2
L.Fir 26:4
sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu.
Explore L.Fir 26:4
3
L.Fir 26:3
“Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su
Explore L.Fir 26:3
4
L.Fir 26:6
“Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba.
Explore L.Fir 26:6
5
L.Fir 26:9
Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.
Explore L.Fir 26:9
6
L.Fir 26:13
Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”
Explore L.Fir 26:13
7
L.Fir 26:11
Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba.
Explore L.Fir 26:11
8
L.Fir 26:1
Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.
Explore L.Fir 26:1
9
L.Fir 26:10
Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da sūnā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo.
Explore L.Fir 26:10
10
L.Fir 26:8
Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.
Explore L.Fir 26:8
11
L.Fir 26:5
Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.
Explore L.Fir 26:5
12
L.Fir 26:7
Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku.
Explore L.Fir 26:7
13
L.Fir 26:2
Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji.
Explore L.Fir 26:2